Latest:
Labarai

Wike ya kori shugabannin hukumomi 21 na Abuja

 

Ministan Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Nyesom Wike, ya sallami shugabannin manyan hukumomi da ma’aikatun Abuja ashirin da daya.

Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Anthony Ogunleye, mai magana da yawun ofishin ministan, ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ba ta fadi dalilan da suka sa ministan ya kori shugabannin ma’aikatun ba. Sai dai tun da aka nada shi a mukamin minista, Mr Wike ya sha alwashin yin garambawul ga ma’aikatun birnin.

Ta kara da cewa an umarci mutanen su mika ragamar ofisoshinsu ga daraktoci mafi girman mukamai na ma’aikatunsu, tana mai cewa nan ba da jimawa za a maye gurbinsu.

Kazalika ya ce zai kawo gagarumin sauyi a birni na Abuja, wanda ya ce ana keta doka a fannoni daban-daban. Hasalima tuni Mr Wike ya soma rusa wasu gine-gine a birnin na Tarayyar Nijeriya, wadanda ya ce an yi su ba bisa ka’ida ba.

Ga jerin ma’aikatun da ministan na Abuja ya kora daga aiki:

Kamfanin Zuba Jari na Abuja

Hukumar Kula da Kasuwannin Abuja

Hukumar Sufuri ta Abuja

Hukumar Samar da Ci-gaban Gidaje da Gine-Gine ta Abuja

Kamfanin Ci-gaban Fasaha na Abuja

Ma’aikatar Fina-finai ta kasa da kasa da ke Abuja

Kamfanin Powernoth AICL Equipment Leasing Ltd

Hukumar Watsa Labarai ta Abuja

Hukumar Abuja Enterprise Agency

Hukumar Samar da Ruwa ta Abuja wato FCT Water Board

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Abuja

Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Abuja

Hukumar Kula da Asibitoci ta Abuja

Hukumar Kula da Muhalli ta Abuja

Hukumar Bayar da Tallafin Karatu ta Abuja

Hukumar kula da Kiristoci Masu zuwa Ziyara wurare masu Tsari

Hukumar Aikin Hajji ta Aabuja

Cibiyar Abuja Infrastructure Investment

Hukumar Inshorar Lafiya ta Abuja

Ma’aikatar da ke Kula da Garuruwan da ke Kewayen Abuja

Majalisar Kula da Cikin Birnin Abuja

TRT Afrika