Labarai

Gwamnatin Tinubu na shirin tsara ƴan Najeriya da farfaganda – Atiku

 

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi zargin cewa, gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ta shirya tsara ‘yan Nijeriya a wasu kwanaki masu zuwa. 

Ya bayyana cewa Tinubu ya nada masu ba shi sharawa a kan fannin yada labarai sama da 15, saboda su dunga fitar da bayanai marasa inganci kan manufofi gwamnati tare da kawar da hankalin ‘yan Nijeriya kan matsanancin halin da gwamnatinsa ta jefa su a ciki.

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya ce labarin karya ne ake yadawa game da dage haramcin biza da kasar Dubai ta yi wa Nijeriya, amma babu kamshin gaskiya cikin lamarin.

Ya ce wannan shi ne salon gwamnatin Tinubu kuma shugaban jam’iyyarsa.

Atiku ya ce, “Daga bayanan da muka samu, Bola Tinubu na shirin tura farfaganda don wuce gona da iri yayin da yake shirin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya. Zai yi ikirarin ya janyo masu zuba jari na kasashen waje da ya kai dala biliyan 100, amma zai kasa bayar da cikakkun bayanai. Wannan duk farfaganda ce. A kasar Indiya, ya yi ikirarin cewa sun karbi hannun jari sama da dala biliyan 14 kamar yadda magabacinsa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a shekarar 2018 cewa ya karbi na dala biliyan 6. Wannan ba komai ba ne illa saka hannun jari na fatar baki.

“A watan da ya gabata, kamfanin NNPC ya yi ikirarin cewa ya samu rancen dala biliyan 3 da zai taimaka wajen daidaita darajar naira. Mun bayyana cewa duk wannan wata dabara ce ta yaudarar ‘yan Nijeriya. Yanzu dai mun tabbatar da cewa naira na kara durkushewa, wanda a yanzu haka dala ta kusan naira1,000 a kasuwar bayan fage.

“Bayan tafiyarsa zuwa Dubai, Tinubu ya yi ikirarin cewa an dage takunkumin haramcin biza nan take. Yanzu haka sun sauya sheka bayan da hukumomin kasar Dubai suka bayyana cewa labarin karya ne. Irin wannan abin kunya ne ga Nijeriya wanda gwamnati ke ci gaba da jawowa a wannan mulki.

“Duk da ya kasa inganta harkokin tattalin arzikin kasa, amma ya nada masu ba shi shawara kan harkokin yada labarai har guda 15, maimakon ya nada masana tattalin arziki.

“Daga cikin jerin masu ba shi shawara kan harkokin yada labarai akwai da sadarwa akwai: Tunde Rahman,Tope Ajayi, Abdulaziz Abdulaziz, Otega Ogara, Segun Dada da Nosa Asemota .

Sauran su ne: Sunday Moses, Taiwo Okonlawon, Moremi Ojudu, Tanko Yakasai, Chioma Nweze, Abiodun Essiet, Abdulhamid Yahaya Abba da kuma Emmanuella Eduozor. Baya ga wadannan akwai kuma ministan yada labarai da suran wasu nade-nade a ma’aikatan domin yada farfaganda.”

Ya bukaci ‘yan Nijeriya su ci gaba da hakuri a daidai lokacin da kotun koli ke shirin zantar da hukunci kan zaben shugaban kasa.

Jaridar Leadership