Latest:
LabaraiNews

Hadarin Mota Ya Kashe Mutum 12 A Jihar Kwara

Akalla mutum 12 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Ilorin zuwa Ogbomosho da ke Jihar Kwara a ranar Asabar.

Aminiya ta rawaito cewa wata mota kirar Toyota Hiace mai cin mutum 18 da ke hanyar zuwa Legas ce ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota kirar Daf.

Fasinjoji shida dai da suka tsira da ransu sun ji raunuka daban-daban a hatsarin da ya faru wajen misalin karfe 7:00 na safe.

Wani ganau ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da direban Hiace din yake tsala gudu a hannun da ba nasa ba.

Kwamandan Shiyya na Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar ta Kwara, Jonathan Owoade, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar hatsarin.

Leave a Reply