Labarai

Najeriya Ce Kasa Ta 11 A Yawan Masu Amfani Da Intanet A Duniya – NCC

 

Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce Najeriya ce kasa ta 11 a yawan masu amfani da intanet a duniya, ta bakwai kuma a yawan masu amfani da wayar salula.

Shugaban hukumar, Farfesa Umar Garba Dambatta ne ya bayyana hakan a yayin bude wani taro kan fasahohin sadarwa na zamani ranar Alhamis a Abuja.

Dambatta, wanda shugaban kamfanin adana bayanai na Spectrum, Abraham Oshadami, ya ce alkaluman da hukumar NIR ta tattara sun nuna yawan amfani da intanet na taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.

Ya ce NIR ta duba kasashe 131 a bangarori hudu da suka hada da kayayyakin fasaha da shugabanci da jama’a da kuma tasirinsu.

Farfesa Dambatta ya ce, “Najeriya cibiya ce ta harkokin sadarwa na zamani, inda kaso 82 na masu amfani da wayoyin hannu na nahiyar Afirka ’yan Najeriya ne, yayin da kaso 29 na masu amfani da intanet a Afirka ’yan Najeriya ne.

“Kasarmu ce ta 11 a duk fadin duniya a fannin amfani da intanet da kuma wayar salula.

“Sai dai duk da wadannan alkaluma da suke zama gwanin ban sha’awa, kasancewar ita ce ta 109 a duniya a karfin netwok daga cikin kasashe 131, babban kalubale ne,” in ji shi.

Aminiya

Leave a Reply