Home Labarai Jirgi mai saukar ungulu na sojin Najeriya ya yi hatsari a Neja

Jirgi mai saukar ungulu na sojin Najeriya ya yi hatsari a Neja

Wani jirgi mai saukar ungulu na rundunar sojin saman Nijeriya ya yi hatsari a kusa da kauyen Chukuba da ke Jihar Neja a yankin tsakiyar kasar.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe daya na rana agogon Nijeriya a ranar Litinin, kamar yadda sanarwar da rundunar sojin saman ta fitar mai dauke da sa hannun daraktan watsa labaranta, Air Commodore Edward Gabkwet, ta bayyana.

“Helikwaftan yana kan hanyarsa ta tafiya Kaduna ne bayan da ya bar Makarantar Firamare ta Zungeru inda daga baya aka gano ya fadi a kauyen Chukuba da ke karkashin karamar hukumar Shiroro,” kamar yadda sanarwar ta ce.

Rundunar ba ta bayar da rahoton ko an rasa rayuka a hatsarin ba, amma ta ce ana aikin ceto matukan jirgin da fasinjojin da ke cikinsa, sannan an kaddamar da binciken farko don gano musabbabin hatsarin.

TRT Afrika Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Discover more from Albarka Radio

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading