Kotun shariar musulunci dake zamanta a Éanbare karkashin jagorancin Mai Shariâa Munzali Idris Gwadabe ta yankewa wani mutum hukuncin Éaurin shekara Éaya Babu zaÉin tara, bayan samunsa da laifin kwashe shinfiÉun masallaci da kuma agogon bango na wani masallaci dake unguwar Æorayi a jihar Kano.
Tunda fari dai ‘Yan sanda ne suka gurfanar da Kabiru Abdullahi ‘yan Æusa bisa kunshin tuhumar shiga waje ba tare da iziniba da sata.
Mai gabatar da Æara Bashir Wada Aliyu ya karanto masa tuhumar, kuma ya amsa laifinsa hakan yasa aka yanke masa hukuncin.
Freedom Radio
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








