Latest:
Labarai

Kotu ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2023

 

Kotun sauraren kararrakin zaben Nijeriya ta tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar a zaben da aka yi na watan Fabrairun 2023.

Kotun wacce ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba a zamanta na karshe na sauraron karar, inda ta yi watsi da korafe-korafen da manyan ‘yan takarar shugabancin kasar a zaben 2023, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na Jam’iyyar LP suka shigar ta neman soke zaben Shugaba Tinubu.

Sai dai Jam’iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin kotun. Sakataren Watsa Labarai na LP Obiora Ifoh ya ce ba a yi adalci ba a shari’ar kuma ba a bi muradun al’umma ba.

“’Yan Nijeriya shaidu kan yadda aka yi fashin zabe ranar 25 ga watan Fabraiun 2023, wanda aka yi Allah wadai da shi a fadin duniya amma Kotun Sauraron Karar Zaben ta yi biris da wannan abu,” ya ce.

Shi kuwa Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin ne a wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan kotun ta sanar, inda ya ce hukuncin ya kara masa azamar daukar nauyin da ya rataya a wuyansa na yi wa ‘yan Nijeriya aiki ba tare da nuna bambanci ba.

Watsi da korafe-korafen da Jam’iyyar Labour ta shigar

An yi watsi da karar da Jam’iyyar LP da dan takararta Peter Obi suka shigar kan zargin cewa an tafka kura-kurai a yayin kada kuri’a, inda kotun ta ce sun gaza yin bayanin yadda suka ce sun yi nasarar samun mafiya yawan halastattun kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun.

A yayin da yake karanto korafe-korafen da ake shari’a a kansu, Mai Shari’a Abba Bello Mohammed ya ce jam’iyyar LP ta yi zargin cewa an tafka kura-kurai da tursasa wa masu zabe da ba da cin hanci don kwace musu kuri’un musamman a jihohin Ribas da Binuwai da Legas da Tarana da Imo da Osun amma ta kasa kawo sunayen rumfunan zaben da aka yi haka din.

Mai Shari’a Mohammed ya karkare da cewa Jam’iyyar LP ta gaza tabbatar da dukkan zarge-zargen da ta yin a aringizon kuri’u da APC ta yi da rage yawan kuriun ita LP din.

Kotun sauraron kararrakin zaben ta kuma yi watsi da bayanan da shaidu 10 cikin 13 da Peter Obi da LP suka gabatar. Alkali Tsammani ya ce bayanan shaidun na rantsuwar da suka yi bas u cancanta ba.

Kotun ta sake yin watsi da bukatar Jam’iyyar Labour da Peter Obi da ke neman a soke zaben Tinubu kan batun kwace dala miliyan 460 a wata Kotun Amurka.

Ta yi watsi da ikirarin Peter Obi da jam’iyyarsa cewa sun samu kashi 25 cikin 100 na jumullar kuri’un Babban Birnin Tarayyar Abuja.

TRT Afrika

Leave a Reply