Siyasa

Kule A Buhu: APC Ta Canza Ranakun Gudanar Da Zabukan Fidda Gwanayen Ta

Cikin wata sanarwa da Kakakin jam’iyyar APC ya fitar ranar Talata, Felix Morka ya ce a sabuwar jadawalin da jam’iyyar ta amince da shi shine cewa za a gudanar da zabukan kujerun yan takarar sanatoci ranar 28 ga watan Mayu.

” Za a gudanar da zabukan kujerun ƴan takarar kujerun ƴan majalisar tarayya ranar 27 ga watan Mayu.

Morka ya ce ranakun da za ayi zaben kujerar dan takarar shugaban kasa na nan daram 29-30 ga watan Mayu.

Sai dai kuma har yanzu jam’iyyar bata sanar da ranar da zata yi zaman tantance ƴan takarar shugaban kasa ba.

Daga cikin waɗanda za’a fafata da su a zaben fidda gwanin na shugaban kasa sun haɗa da gwamnan Jigawa Mohammed Badaru, Tsohon gwamnan Legas, Sanata Bola Tinubu, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, mataimakin shugaban kasa , Yemi Osinbajo, shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan , da dai sauran su.

Leave a Reply