Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ ta ce za ta bi sahun Æungiyar Kwadago ta NLC a Æasar wajen tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba mai zuwa, saboda cire tallafin man fertur.
Æungiyar ta bayyana cikin wata takarda da ta fitar, bayan ganawar da kwamtin gudanarwarta ya yi da safiyar ranar Asabar domin tattauna batun cire tallafin man fetur da gwamnatin Æasar ta yi da kuma matakin Æungiyar Æwadago ta NLC ta Éauka na shiga yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.
Æungiyar ta NUJ ta ce a halin da ake ciki tashin farashin man fetur da na sauran kayayyaki sun jefa al’ummar Æasar cikin mawuyacin hali.

Haka kuma Æungiyar ta umarci mambobinta da ke faÉin jihohin Æasar da su fara yajin aiki tare da fita zanga-zanga daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni matuÆar kamfanin mai na Æasar NNPCL bai janye Æarin farashin man fetur da ya yi ba.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








