Labarai

Kungiyar Izala Ta Aurar Da ‘Yan Mata Marayu A Abuja

A Ranar Laraba Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah reshen babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ya gudanar da auren ‘yan mata marayu guda 20.

Kwamitin kungiyar na babban birnin shi ne ya shirya bikin daurin auren a karkashin inuwar kungiyar ta kasa. Bayan daura auren an bai wa ma’auratan kayan daki da jari na tsabar kudi domin yin sana’a.

Ga hotunan yadda bikin ya wakana daga masallacin Berger da ke Unguwar Utako ranar 24 ga watan Agustan 2022.

Leave a Reply