Labarai

Dubban Mutane Sun Makale Saboda Rikici A Sudan Ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa dubban mutane sun makale a Sudan ta Kudu sakamakon mummunan rikicin da ake tsakanin kungiyoyin masu tayar da kayar baya a kasar.

Kazalika ambaliyar ruwan da aka samu a arewacin kasar da ta yi sanadin mutuwar gwamman mutane ma ta assasa tserewarsu daga in da suke.

Tun bayan fara rikicin kwanakin 10 da suka wuce a garin Tonga da ke arewacin kasar,Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane kusan 200 ne suka samu damar tserewa zuwa Malakal.

Rahotanni sun ce ba a san abin da ya assasa rikicin ba, to amma kasar na fama da rikicin kabilanci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai fargabar cewa rikicin na iya shafar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a 2018 wadda ta kawo karshe yakin basasar da aka shafe shekaru fiye da 60 ana yi a kasar.

Leave a Reply