An kashe âyan sanda uku a wani hari da wasu da ake zargin âyan bindiga ne suka kai ofishin âyan sanda da ke Karamar Hukumar Adavi ta Jihar Kogi da sanyin safiyar Asabar.
Rundunar âYan Sandan Jihar Kogi ta ce bata-garin sun far wa ofishin ne ta dama da hagu suna harbi babu kakkautawa, amma âyan sanda suka fatattake su.
âAbin takaici, âyan sanda uku sun rasu a musayar wutar, bata-garin kuma suka tsere da raunukan harbi a jikinsu ba tare da sun samu shiga ofishin âyan sandan ba,â inji kakakin rundunar, SP William Ovye.
Sanarwar da ya fitar a safiyar Asabar ta ce Kwamishinan âYan Sandan Jihar Kogi, Edward Egbuka, ya tura jamiâai na musamman don tabbar da doka da oda a yankin tare da kamo maharan su girbi abin da suka shuka.
SP Ovye ya bukaci mazauna yankin da makwabtansu da su sa ido sosai, duk wanda suka gani da raunin harbi su hanzarta sanar da jamiâan tsaro.
Ya ce kwamishinan âyan sandan jihar ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike nan take, bisa jagorancin Mataimakin Kwamishian âYan Sanda Mai Kula da Binciken Manyan Laifuka.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








