Labarai

Majalisa ta shiga zaman sirri saboda sa’insa a kan tantance Festus Keyamo

 

Sanata Darlington Nwokocha ne ya fara gabatar da ƙudirin haka a gaban majalisa, inda ya nemi a dakatar da shi har sai lokacin da ya amince da cewa majalisa na da damar bincikar ayyukan ministoci.

Hakan ya faru ne sakmakon tirjiyar da ya nuna a lokacin da yake minista a baya, inda ya ƙi amsa gayyatar majalisa.

Ƙudirin ya samu goyon bayan mafi rinjayen sanatoci, hakan ya sa daga ƙarshe majalisar ta yanke shawarar shiga zaman sirri kan lamarin.

Festus Keyamo shine ministan gwamnatin Buhari da ya sake shiga cikin jerin sunayen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin minista.

BBC Hausa

Leave a Reply