A jamhuriyar Nijar, wa’adin da Æungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin da sukai juyin mulki a Jamhuriyar Nijar na su koma barikokinsu da maida mulki ga farar hula ko su Éauki matakin soji, ya cika ba tare da sun bi umarnin ba.
Gwamnatin sojin Nijar ta sanar da rufe sararin samaniyar Æasar, da kuma shirin kare iyakokin Æasar na kasa. Wakiliyar BBC ta ce “Mun sa ran kungiyar Ecowas za ta fitar da wata sanarwa daidai lokacin da wa’adin ya cika, ko matakin da za ta dauka nan gaba, amma shiru ka ke ji.”
Kawunan mambobin Æungiyar ECOWAS ya rarrabu kan Éaukar matakin sojin, inda Nigeria da Ivory Coast suka kafe kan lallai a dawo da mulki hannun shugaba Muhammad Bazoum, su kuwa Mali da Burkina Faso ke goyon bayan sojojin da sukai juyin mulkin.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








