Wani rahoto na kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a Najeriya ya ce Æ´an bindiga sun hallaka mutum 1,715 a faÉin Najeriya tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2023.
A cikin rahoton wanda kamfanin ya fitar yau Alhamis, ya ce an kashe mutane mafi yawa ne a yankin arewa maso gabashin Æasar, inda aka kashe mutum 491.
Sai kuma yankin arewa masotsakiyar Æasar inda aka kashe mutum 366.
Arewa maso yammacin Æasar ne na uku a yawna mutanen da aka kashe, inda aka kashe mutum 362.
Jihohin da lamarin ya fi muni su ne Borno da Filato da kuma Zamfara.
Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro a yankunan daban-daban na Æasar, waÉanda suka haÉa da na Æ´an fashin daji a arewa maso gabas da Boko Haram a arewa maso gabashin Æasar.
Bugu da Æari ana fama da matsalar Æ´an fashi da kuma masu garkuwa da mutane a arewa maso tsakiya da kuma kudancin Æasar.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









