Latest:
Labarai

Najeriya Za Ta Iya Cigaba Da Ciwo Bashi Har Abada – Adamu Abdullahi

Shugaba jam’iyyar APC na Kasa, Adamu Abdullahi ya bayyana cewa Najeriya za ta iya cigaba da ciwo bashi daga kasashen waje daga yanzu har tashin duniya, babu komai.

Shugaba Abdullahi ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da Talbijin din Trust TV.

Wannan kalamai na Abdullahi Adamu ya zo a daidai Hukumar IMF ta yi gargadin cewa idan Najeriya bata taka birki a ciwo basussuka da take yi ba, karshenta za ta rika kawashe kudaden shigan ta ne kaf tana biyan basussuka da su babu abinda za ta iya aiwatar wa na cigaba kuma zuwa 2026.

Zuwa yanzu ana bin Najeriya bashin sama da naira Tiriliyan 41, da suka hada da basussukan da ake ci tun daga kananan hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya, kuma a gwamnatin Buhari ne aka ciwo mafi yawan bashi a Najeriya.

“Ni fa ban ga wani abin tashin hankali a ciwo bashi ba. Kasashen da suka cigaba ma suna cin bashi domin gina ababen more rayuwa a kasashen su.

” Ni fa bani da matsala da cin bashi. Gwamnati za ta iya cigaba da rankato bashi ta kowacce hanye har abada, ba ni da matsala da haka. domin na sha fadin haka.

” Kasashen Amurka, Canada, UK, faransa duk suna cin bashi daga bankin duniya, don Najeriya ita ma ta karbo bashin ina laifi yake a ciki.

Leave a Reply