Latest:
LabaraiWorld News

Shugaba Buhari Ya Taya Shugaban Kasar Faransa Macron Murnar Lashe Zaɓe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron murnar lashe zaɓe wa’adi na biyu.

Shugaban ya ce akwai kyakykyawar alaƙa tsakanin Najeriya da kasar Faransa tun bayan hawan shugaba Macron a shekarar 2017, inda ya kai ziyarar aiki Najeriya a shekarar 2018.

Ya kuma ce shugaban ya samar da hanyoyi na inganta alaƙar tattalin arziki da al’adu da tsaro tsakanin Najeriya da Faransa musamman a taron Faransa da kasaahen Afirka.

Leave a Reply