Shugaba Bola Tinubu na duba yiwuwar dawo da bayar da tallafin man fetur na dan wucin gadi biyo bayan matsin rayuwa da aka shiga da kuma yadda farashin Dalar Amurka ke ta hauhawa tun bayan cire tallafin a watan Mayu, Inji jaridar The cable
Har yanzu dai shugaban bai tabbatar da wannan kuduri ba amma takardar shawarar tana kan teburinsa, kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa TheCable.
Tuni dai kungiyoyin kwadago suka yi barazanar shiga yajin aiki na sai Baba-ta-gani idan farashin man fetur ya kara hauhawa.
Leadership Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.