Labarai

Wani ɗan haya ya yi fyaɗe wa ƴar Fasto ta dauki ciki

 

Wani dan haya ya shiga hannun hukuma kan zargin yi wa ’yar mai gidan da yake zaune a ciki fyade kuma ta dauki juna biyu.

Faston ya shaida wa kotun hukunta laifukan fyade ta Jihar Legas cewa magidancin ya shafe sama da shekara biyu yana lalata da yarinyar, har ta dauki ciki ta haihu.

Ya ce abin takaicin shi ne matar dan hayan, wadda ma’aikaciyar jinya ce, ta ba wa yarinyar maganin zubar da ciki, don kar asirin mijin nata ya tuno.

“’Yata ta bayyana cewa shi ya yi mata ciki, kuma tun shekarar 2021 yake lalata da ita.

Ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake amsa tambayoyin lauyan magidancin da ake zargi a gaban kotu.

“Na gamsu cewa shi ne ya yi wa ’yata ciki, kuma matarsa ce ta ba yarinyar maganin zubar da ciki,” inda daga baya ya kai kara ofishin hukumta laifukan jima’i.

Kotu ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Disamba.

Jaridar Aminiya