Labarai

’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane A Masallacin Juma’a A Jahar Zamfara.

’Yan bindiga sun kai wa masu Sallar Juma’a hari, inda suka sace mutane da dama a Karamar Hukumar Gummi ta Jihar Zamfara.

Maharan sun boye bindigoginsu a jikinsu sannan suka saci jiki suka shiga cikin masallata a ciki da wajen masallacin a yayin da liman ke daf da fara hudumar Juma’a, a masallacin da ke unguwar Zugu.

Daga baya sai suka umarci mutanen da ke harabar masallacin da su shiga cikin ginin masallacin.

Bayan sun mamaye masallacin suka fito da bindigoginsu cewa sun zo ne domin a tattauna su sako mutanen da suka sace.

Wani mazaunin yankin, Abubakar, ya ce, “Babu wanda ya gan su rike da bindiga, an zaci Sallah suka zo, saboda haka babu wanda ya damu da su, saboda sun boye bindigoginsu.

“Amma bayan sun shiga cikin masallacin sai suka fiffito da bindigoginsu suka yi harbin razana jama’a.

“Daga nan suka wuce da wasu mutane da ke masallacin, har da ladanin zuwa cikin daji, amma wasu mutanen da ke masallacin sun samu sun tsere, ciki har da limamin.

“Mutanen da ke harabar masallacin ma an tafi da wasunsu, saboda ba su sani ba a ashe wasu daga cikin ’yan bindigar sun tsaya a waje sun kama wuri; Sai da suka yi ta harbi a iska kafin su kora mutanen zuwa cikin daji.

Zuwa lokacin da muka kammala wannan rahoton, kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce bai samu labarin harin ba tukuna, amma ya yi alkawarin idan ya samu zai waiwayi wakilin namu.

Leave a Reply