Kimanin ‘yan ta’addan Boko Haram 78 ne suka mika wuya ga dakarun soji a karamar hukumar Monguno ta jihar Borno.
An bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun mika wuya ne sakamakon farmakin da sojoji suka ci gaba da kai wa maboyarsu da kuma fada da ‘yan ta’addar ISWAP da ke gaba da juna, wanda ya kai ga kashe ‘yan ta’adda sama da 100 daga bangarorin biyu a cikin kwanaki bakwai da suka gabata.
Kungiyoyin biyu suna amfani da karfinsu wajen kai wa juna hari.
A mafi yawan lokuta, suna kai hari ga kan uwa da mai wabi, ciki har da mata da yara.
Wasu bayanai da aka samu daga majiyoyin leken asiri da kuma wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa mayakan sun zubar da makamansu bayan hare-haren sojoji.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, a ranar 13 ga watan Agusta, 2023, kungiyar Boko Haram ta kama ‘yan ta’addar ISWAP kimanin 60 da suka hada da wasu manyan kwamandoji uku Abubakar Saddiq, Abou Maimuna da Malam Idris, a hanyarsu ta zuwa Damasak.
Daga baya sun kai manyan da suka aka kama zuwa wani gidan yari da ke Kwatan Mota kusa da Dogon Chuku, inda ake tsare da su a matsayin fursunonin yaki.
Leadership Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.