Labarai

Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu Wa Dokar Kara Kudin Kiran Waya

Shugaban kasa Muhammadu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar karin kudaden haraji ga masu kiran waya a kasa baki daya.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar, inda ta ce za’a yi karin kwabo guda kan kowanne kira da dan Najeriya zai yi, kari kan abinda aka saba biya.

Ta cikin sanarwar fadar shugaban Najeriyar ta ce za’a yi amfani da kudaden ne wajen taimakawa gajiyayyu da kuma zuba su don tsamo tattalin arzikin kasar daga mawuyacin halin da yake ciki.

Ko da sanarwar ta ci gaba da karin bayani ta ce za’a fi karkata kudaden ne ga bangaren lafiyar gajiyayyu da masu bukata ta musamman don inganta lafiyar su.

Tuni dai ‘yan Najeriya suka fara yiwa sabuwar dokar bore, a ganin su halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki kamata ya yi a ragewa dan Najeriya harajin da yake biya ba wai kara masa ba.

Leave a Reply