Latest:
Labarai

An bukaci gwamnatin jihar Bauchi da ta tallafawa ƴan gudun hijira dake samun mafaka a ƙaramar hukumar Tafawa Balewa

Daga Muhammad Adamu 

Akalla ‘yan gudun hijira sama da 2,000 ke zaman gudun hijira a sakamakon rikicin kabilanci a Mangun Jihar Filato a yanzu haka ke samun mafaka a karamar hukumar Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi.

Shugaban kwamatin riko na karamar hukumar Tafawa Balewa Sama’ila Wakili, wanda ya kai ziyarar aiki a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke makarantun firamare na Boto da Lere, ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa da ke bukatar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ta dauki matakin gaggawa.

Sama’ila Wakili ya jajanta musu bisa faruwar lamarin, ya kuma bayar da tallafin kayayyakin agaji na Naira miliyan 2.5 domin saukaka musu cikin gaggawa.

Yace, rikice-rikicen ya shafi mata da kananan yara wadanda da yawa daga cikinsu sun zama zawarawa da marayu, yayin da wasu da dama kuma suka rasa dukiyoyinsu.

Daga cikin kayayyakin Da aka bayar sun hada da taburmai, bokatai, garri, sukari, kofuna da kuma butan roba, sannan kuma sai ya yi alkawarin samar musu da bandakuna domin gujewa barkewar wata cuta da kuma kaucewa yin bahaya a fili.

A nasa jawabin, Daraktan Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Bauchi SEMA Bala Tafida, ya ce sun ziyarci sansanonin ne domin tantance adadin ‘yan gudun hijirar tare da tattara bayanansu kan yadda za a taimaka musu.

A nasu bangaren, shugabannin ‘yan gudun hijirar Manu Mohammed da Raihanatu Musa, sun roki gwamnatin jihar Bauchi, kungiyoyi gamida masu hannu da shuni da su kawo musu dauki domin suna cikin halin yunwa da kuma rashin kayan amfanin bayan gida a sansanoninsu.

Leave a Reply