Labarai

Cikin Shekaru huɗu Majalisar Dokokin jihar Bauchi tayi dokoki 105 cewar Kakakin Majalisar 

Daga Jibrin Hussaini Kundum

 

Kakakin Majalisar dokokin jihar Bauchi Abubakar Y. Sulaiman yace cikin shekaru hudu na Majalisar jiha ta aiwatar da dokoki 105 tare da kudirin dokoki 131 hadi da bukatun al’umma dasuke bukatar agaji cikin gaggawa guda 93.

Ya bayyana hakane yayin zaman karshe da Majalisa ta 9 tayi daya wakana a zauren Majalisar dokokin jihar ta Bauchi.

Kakakin Majalisar yagano cewar ansamu kyakkyawar dangantaka tsakanin bangaren majalisar da bangaren zartaswa ta jihar Bauchi wanda hakan ya inganta rayuwar al’ummar jihar.

Yakuma yaba da kokarin manyan shugabannin Majalisar bisa mara mishi baya da sukayi batare da wani chikas ba.

Cikin jawaban su daban-daban Mataimakin kakakin Majalisar Danlami Ahmad Kawule da shugaban masu rinjaye na Majalisa ta 9 duk’kan su sun bukaci za6a66un mambobin majalisa ta goma da suyi aiki tukuru domin sauke nauyin mazabunsu.

Leave a Reply