Labarai

Dino Melaye Ya Sha Kasa A Zaben Fidda Gwani Na Sanata A Kogi

Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye ya sha kase a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a yunkurinsa na sake komawa kan kujerar.

Sanata Dino dai ya sha kayen ne a hannun abokin takararsa, Teejay Yusuf, wanda ya sami kuri’u 163, shi kuma Dino ya sami kuri’a 99 a zaben da aka gudanar ranar Talata.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaben, wanda ya sami nasarar, wanda kuma dan Majalisar Wakilai ne mai ci da ke wakiltar mazabar Kabba/Bunu ya ce nasarar da ya samu iko ne na Allah.

Kazalika, ya kai ziyarar godiya da ban gajiya ga jagororin mazabar na Kogi ta Yamma bisa gudummawar da suka ba shi a nasarar da ya samu na zama dan takarar Sanatan a PDP.

Ya kuma yaba wa daliget-daliget na jam’iyyar bisa zabarsa da suka yi, tare da bayyana cewa zai ci gaba da ba su girmansu kamar yadda ya kamata.

Leave a Reply