LabaraiSiyasa

Duk ‘Deliget’ Din Dake Jiran In Bashi Kuɗi Ya Taka ‘Zero – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa ba zai janye daga takarar gwamnan ba amma kuma wakilai wato ‘Deliget’ su sani ba zai basu ko sisi ba.

“Ba zan ba ɗeliget ko sisi don su zaɓe ni ba, hakan baya cikin tsarin siyasa ta, kuma bana buƙatar wani ya ba su kudi don ni.

” Masu kira na don in basu miliyoyin kuɗi sun taka zero domin ko sisi ba zan basu ba. Wanda ya yarda da tafiyata ya kuma amince da manufofi na ya zabe ni, amma ba zan ba da ko sisi ba.

Shehu Sani ya ce idan zai faɗi zabe gara ya fadi da mutuncin sa.

Shi kuwa wanda ya mallaki jami’ar Baze dake Abuja, kuma ɗan takarar gwamnan Kaduna, Datti Baba-Ahmed ya janye daga takar gwamnan jihar Kaduna.

Baba-Ahmed ya fito takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Sai dai kuma yanzu da zaben fidda gwani ya matso gaban goshi, tsohon sanatan ya ce ya janye daga takarar gwamnan saboda kuɗi.

” Na janye daga takarar gwamnan Kaduna saboda gaba daya abinda na ke gani ba abu bane wanda ke nuna muna so a kawo sauyi ta gari a kasar nan. Kwamacalar da aka saba dai ita ce ake yin har yanzu tun daga zaben fidda ƴan takara dake gudana yanzu haka.

” A dalilin haka na hakura na janye daga takarar gwamnan jihar.

Leave a Reply