Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa ba zai janye daga takarar gwamnan ba amma kuma wakilai wato âDeligetâ su sani ba zai basu ko sisi ba.
âBa zan ba Éeliget ko sisi don su zaÉe ni ba, hakan baya cikin tsarin siyasa ta, kuma bana buÆatar wani ya ba su kudi don ni.
â Masu kira na don in basu miliyoyin kuÉi sun taka zero domin ko sisi ba zan basu ba. Wanda ya yarda da tafiyata ya kuma amince da manufofi na ya zabe ni, amma ba zan ba da ko sisi ba.
Shehu Sani ya ce idan zai faÉi zabe gara ya fadi da mutuncin sa.
Shi kuwa wanda ya mallaki jamiâar Baze dake Abuja, kuma Éan takarar gwamnan Kaduna, Datti Baba-Ahmed ya janye daga takar gwamnan jihar Kaduna.
Baba-Ahmed ya fito takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwar jamâiyyar PDP.
Sai dai kuma yanzu da zaben fidda gwani ya matso gaban goshi, tsohon sanatan ya ce ya janye daga takarar gwamnan saboda kuÉi.
â Na janye daga takarar gwamnan Kaduna saboda gaba daya abinda na ke gani ba abu bane wanda ke nuna muna so a kawo sauyi ta gari a kasar nan. Kwamacalar da aka saba dai ita ce ake yin har yanzu tun daga zaben fidda Æ´an takara dake gudana yanzu haka.
â A dalilin haka na hakura na janye daga takarar gwamnan jihar.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








