Abdul Tech Systems Ltd
Labarai

Jami’an Tsaro Nigeriya Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu Da Ke Kaduna

Published by Zainab Sabitu

Jami’an tsaro – wadanda ake kyautata zaton jami’an hukumar ‘yan sandan farin kaya ta DSS ne – a Najeriya sun kai samame gidan Tukur Mamu, mutumin da ke shiga tsakani da ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa na Kaduna.

Wasu mazauna unguwar sun tabbatar wa da BBC cewa jami’an tsaron sun isa gidan ne da ke Kaduna a motoci kimanin 10 da sanyin safiyar yau Alhamis, inda suka yi awon gaba da wasu kayyayaki.

Tukur Mamu dai shi ne mutumin da ke shiga tsakanin ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa a Kaduna da kuma iyalansu domin kubutar da su. Fasinjojin da aka kubutar daga hannun ‘yan bindigar kan fara zuwa ofishinsa da farko, kafin su hadu da iyalansu.

A jiya ne dai ‘yan sandan kasa da kasa na kasar a Masar suka kama Tukur Mamu a filin jirgin saman a birnin Al-khahira, lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya.

Hakan na zuwa ne bayan rundunar soji, da fannin shari’a sun bukaci abokan huldarsu na kasashen waje su dawo da Mamu gida domin amsa tarin tambayoyin da jami’an tsaron Najeriya ke son ya amsa musu, masu alaka da batutuwan tsaro da kasar ke fama da su.

🤞 Don’t miss any Article!

We don’t spam! Read more in our Privacy Policy.

Oh hi there 👋
Don't miss anything.

Sign up to receive awesome content in your inbox.

We don’t spam! Read our Privacy Policy for more info.

About the author

Zainab Sabitu

I'm who I am and that's just enough.
I'm definitely the best of my kind.
Just take a seat and grab a cookie.

Leave a Comment