Latest:
Labarai

Kwamandan Boko Haram, Bulama Bukar ya miƙa wuya ga sojin Najeriya 

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce wani fitaccen kwamandan ƴan ta’addar Boko Haram, mai suna Bulama Bukar, ya mika kansa ga dakarun Runduna ta 5 da ke Gubio a jihar Borno.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brigediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a jiya Laraba a Abuja.

Nwachukwu ya ce dan ta’addan da ya mika wuya shi ne kwamandan BHT Camp Tapkin Chad da ke kauyen Gilima a karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.

“Kayayyakin da aka karɓe daga hannun ‘yan ta’addan da suka mika wuya sun hada da bindiga kirar AK 47 guda daya, gidan jera harsashi 5, harsashi na musamman mai girman 44mm 7.62mm, jaket din dakon gidan jera harsashi daya, wuka daya, babur daya da kuma kudi Naira dubu 23,500.

Ya kara da cewa “A halin yanzu Bukar yana fuskantar tambayoyi domin samun bayanan sirri”.

Daily Nigerian Hausa