Labarai

Satar Langa-Langa Ta Jawo Wa Lebura Daurin Wata 6

Wata kotun addinin Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari a Kaduna ta yanke ma wani lebura daurin wata shida, bisa samunsa da laifin satar fallen langa-langa 11.

An sami leburan mai suna Abdullahi Adamu da laifin satar a Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na Kaduna (KAEDCO).

Tuni dai ya amsa laifinsa, inda ya ce sharrin zuciya ne ya kai shi ga aikata hakan, tare da rokon sassauci daga alkali.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Ma Shari’a Rilwanu Kyaudai ya ba wa mai laifin zabin biyan tarar naira N6,000, tare da umarnin biyan KAEDCO diyyar N25,000.

Tun da fari dai dan sanda mai shigar da kara, insfekta Shu’aibu Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa, “A ranar 19 ga watan Afrilun da muke ciki ne da misalin karfe 8:30 na safe Malam Jibril Adamu jami’in kamfanin KAEDCO ya kai rahoton ga ofishin ’yan sandan Magajin Gari da ke Kaduna, inda ya ce ya kama leburan da langa-langa 11 na kamfanin.”

Laifin, a cewar lauyan, ya ci karo da sashi na 130 na Kundin Penal Code na Jihar ta Kaduna.

Leave a Reply