Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta sake kama mutum 57 da zargin satar kayayyakin jama’a a matsayin “ganima” yayin da gwamnatin jihar ke rushe-rushen gine-gine.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Juma’a ta ce Kwamashinan ‘Yan Sanda Mohammed Usaini Gumel ne ya ba da umarnin yin fatiro babu dare ba rana don kare dukiyoyin mazauna jihar.
A farkon makon nan ma rundunar ta kama wasu mutane, akasarinsu matasa, da zargin fasawa tare da sace kayayyaki a shagunan da ke ginin tsohuwar jaridar Triumph a ƙwaryar birnin Kano.
Lamarin na faruwa ne yayin da sabuwar gwamnatin Kano ƙarƙashin jam’iyyar NNPP ke rushe gine-ginen da ta ce an yi su a kan filayen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta sayar.
A farkon makon nan wasu hotuna da bidiyo suka karaɗe shafukan sada zumunta, inda suke nuna wani gini yana ruftawa da matasa suna tsaka da ɗibar rodina da ƙarafa na wani ginin da gwamnati ta rusa.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.