Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta cafke wani kasurgumin mai safarar kwayoyin da ake zargin na da alaka da dakataccen jami’in dan sandan nan, DCP Abba Kyari.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Litinin, inda ta ce ta kama Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, shugaban kamfanin Mallinson Group bisa safarar kwayar Tramadol ta Naira biliyan uku.
Sanarwar ta ce, “Bayan ya kwashe wata da watanni yana zille wa kamu, an kama Ukata, wanda shi ne Shugaban rukunin kamfanin Mallinson Group, a filin jirgin saman Legas da ke Ikeja a kan hanyarsa ta zuwa Abuja ranar 13 ga watan Afrilu.”
Sanarwar dai na dauke da sa hannun kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi.
Bincike ya nuna cewa shi ne babban mai safarar miyagun kwayoyi nau’i daban-daban kamar Tramadol, hydrochloride mai nauyin kilogiram 120, da 200, 225 da kuma 250 wadanda aka haramta, kamar yadda sanarwar ta fitar.
NDLEA ta ce Ukata yana da kamfanin hada magunguna da kuma na robobi da yake amfani da su wajen yin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasashen ketare.
“Mun soma sanya idanu a kan Ukata ne a shekarar da ta gabata, bayan an kwace katon biyar na kwayar Tramadol mai nauyin kilogiram 225 daga wurin wani ma’aikacinsa a ranar hudu ga watam Mayun 2021, lokacin da ya sayar da ita ga ’yan sandan bad-da-kama na IRT da Kyari ya jagoranta a Ikeja Jihar Lagos,” inji Babafemi.
Tuni dai hukumar NDLEA ta kama Abba Kyari sakamakon wani faifan bidiyo da ta saki wanda ya nuna jami’in na dan sandan yana kulla yarjejeniyar rashawa kan wata hodar Iblis da suka kwace.
Hakan ya sanya Kyari fuskantar shari’a a yanzu, wanda kuma kotu ta hana ba da belinsa.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.