Latest:
Labarai

Rundunar ƴan sandan Bauchi da Kano sun magantu kan zargin masu ‘shan jini’

 

Rundunar ‘yan sandan Bauchi da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta karyata labaran da ake yadawa cewa wasu mata na shiga gidajen jama’a suna shan jininsu.

Ita ma takwararta ta jihar Kano ta yi magana a kan batun amma ta ce tana gudanar da bincike.

A tattaunawarsa da TRT Afrika, kakakin ‘yan sandan Jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakil ya karyata rahotannin da ake yadawa a soshiyal midiya cewa wasu mutum 20 da ake zargi da maita sun shiga Bauchi kuma suna shan jinin jama’a.

Ya bayar da misali da wata mata da bidiyonta ya karade shafukan sada zumunta wadda aka yi zargin tana maita, yana mai cewa ba haka lamarin yake ba.

“Matar mai suna Siddika, mazauniyar Unguwar Shekal ce, ta je wata unguwa mai suna Bakin Kura a cikin garin Bauchi domin neman sadaka, sai ta fadi saboda yunwa.

“Sai wasu mata da matasa suka fara jifanta da duwatsu, suna mai cewa mayya ce,” in ji SP Wakil.

Ya bayyana cewa bayan sun samu wannan labarin sai Kwamishinan ‘yan sandan Bauchi CP Auwwal Musa Mohammad ya bayar da umarni aka yi gaggawar ceto matar.

“Binciken da muka yi ya nuna matar tana da tabin-hankali amma ba mayya ba ce kuma mun mika ta hannun iyalanta,” in ji shi.

SP Wakil ya bukaci jama’a su daina yada jita-jita ko abin da ba su tabbatar da sahihancinsa ba.

Bincike

A Jihar Kano ma, an samu makamancin wannan lamarin na Jihar Bauchi inda wani bidiyo ke yawo wanda ya nuna ana dukan wasu mata kan zargin cewa ‘yan shan jini ne.

Haka ma akwai wasu hotuna da ake yadawa na wata mata wadda aka kama a Karamar Hukumar Gezawa wadda aka yi zargin ta sha jinin matar gidan.

Duk da dai bai tabbatar da lamarin ya faru ko bai faru ba, mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce suna gudanar da bincike kan wadannan lamuran.

TRT Afrika Hausa

Leave a Reply