Labarai

Sojojin mulkin Nijar sun kama malaman jami’a kan nuna adawa da juyin mulki

 

wasu malaman jami’a sakamakon nuna adawa da juyin mulkin da suka yi a watan Yulin da ya gabata.

An kama malaman ne bayan wasu 37 sun nisanta kansu ne daga wata sanarwa da uwar ƙungiyarsu ta fitar da ke ayyana goyon baya ga juyin milkin.

Shugaban majalisar mulkin sojan, Janar Abdourahmane Tciani, ya saka hannu kan wani umarni da ya cire malaman 37 daga duk wani muƙami da suke riƙe da shi a ƙungiyoyinsu.

Kazalika, daga bisani jami’an tsaro suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu.

Tuni dai kungiyoyin fararen hula a kasar suka fara tsokaci kan wannan batu, inda suke kiran da a saki malaman nan take ba tare da sharaɗi ba.

BBC Hausa

Leave a Reply