Labarai

Wani Matashi ya kashe mahaifinsa da taɓarya a Ribas

Wani matashi ya kashe mahaifinsa ta hanyar bugun sa da tabarya a kai a Karamar Hukumar Obio Akpo ta Jihar Ribas.

Aminiya a gano saurain ya yi wannan aika-aika ne bayan da ya bukaci mahaifin nasa ya ba shi kudi, amma mahaifin ya ki garin Rumuaghaolu da ke karamar hukumar.

Hakan ne ya fusata shi, ya je ya dauko tabarya ya rafka wa mahaifin nasa a ka, shi kuma nan take ya ce ga garinku nan.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa, “rashin ba shi kudin da mahaifin ya yi ne fusata shi, shi ne ya buga masa tabarya a ka.

“Ana zargin yaron ya riga ya yi shaye-shaye a lokacin da ya yi wannan aika-aika,” in ji shi.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe Koko ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce wanda ake zargin ya shiga hannu, ana masa tambayoyi.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply