Latest:
Labarai

Zamu haɗa kai da gwamnoni don tantance bayanan talakawan Najeriya – Edu

Ministar harkokin jin-ƙai da kawar da talauci ta Najeriya, Betta Edu ta ce gwamnatin ƙasar za ta yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da gwamnonin jihohi, da ƙananan hukumomi da kuma shugabannin al’umma domin tantance cikakkun bayanan talakawan ƙasar.

Misis Edu ta bayyana haka ne ranar Juma’a a lokacin hira da gidan talbijin na Channels.

Ta ƙara da cewa gwamnati za ta yi hakan ne domin cimma burin ma’aikatar jin-ƙai ta ƙasar na fitar da miliyoyin ‘yan ƙasar daga ƙangin talauci.

”Abu na farko da za mu fara yi, shi ne tantance rajistar sunayen masu ƙaramin ƙarfi ta ƙasar, domin tabbatar da cewa talakawan ne a cikinta, waɗanda suka cancanci shiga cikin rajistar,” in ji Ministar jin -ƙayin.

Ta ci gaba da cewa a ‘yan makonnin baya-bayan nan an yi ta samun ce-ce-ku-ce daga ɓangaren ƙungiyar gamnonin ƙasar da sauran ƙungiyoyi, kan ingancin rajistar.

“Wasu na cewa ta yi, wasu kuma na cewa ba ta ba, saboda mutanen da ke cikinta, ba su ne suka cancanci shiga cikinta ba, an shigar da siyasa cikin wajen haɗa rajistar”, in ji ta.

BBC Hausa

Leave a Reply