Labarai

Shugaba Kasa Buhari Zai Tafi Kasar Rwanda

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai halarci taron shugabannin ƙungiyar Commonwealth ta ƙasashe rainon Ingila da ke gudana a ƙasar Rwanda daga 20 zuwa 26 ga watan Yuni.

Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a yau Laraba ta ce shugaban zai halarci buɗe bikin a hukumance ranar Juma’a.

Taron mai laƙabin CHOGM 2022, zai tattauna kan halin rayuwa da kuma ci gaban al’ummar ƙungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ƙasa 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka da Turai da kuma yankin Pacific.

Ministci da manyan jami’an gwamnatin Najeriya takwas ne za su yi wa Buhari rakiya zuwa Rwanda.

Ana sa ran shugaban zai koma Najeriya ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni.

Leave a Reply