Labarai

Gwamnati ta yi kira ga ƴan Najeriya Su Koma Amfani Da Keke

 

Gwamnatin Najeriya ta bukaci ’yan kasar su koma amfani da keke a matsayin hanyar sufuri da nufin kawar da fitar da gurbatacciyar iska da ke gurbata muhalli.

Wannan kiran na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke kokawa game da tsadar man fetur mafiya yawa a cikin kasa da wata biyu a kasar, bayan janye tallafin da gwamanti take bayarwa.

Darektan Gudanarwar Sufuri da Jigila a Kan Hanyoyi, Musa Ibrahim, ya bayyana wa wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja cewa hakan zai samar da karin fahimta da kuma bunkasa amfani da kekuna a tsakanin ’yan Najeriya.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kamfanin Ochenuell Mobility kuma mai rajin kare harkar sufuri mara fitar da hayaki, Emannuel John, ya ce alfanun tuka keke ya wuce batun kare muhalli ko hanyar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

A cewarsa, binciken hukumar hadakar bunkasa tattalin arziki (OECD) ya nuna cewa a kowace shekaka yawancin kasashen Afirka suna yin asarar kashi 3 cikin 100 na dukiyar da ake samarwa a cikin gida a sakamakon cinkoson ababen hawa.

Don haka ya jaddada muhimmancin amfani da tsarin sufuri mara hayaki domin magance wadannan matsaloli.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply