Lauyan kare hakkokin bil’adama Femi Falana ya bayyana matakin kamfanin mai ta ƙasa NNPCL na ƙara farashin litar mai a matsayin saɓa doka.
Yayi jawabi ne a gefen taron gaggawa da ƙungiyar ƙwadago tayi da majalisar zartaswar ta a birnin tarayya Abuja.
Mista Falana yace kamfanin NNPCL a matsayinsa na kamfani mai zaman kansa a yanzu bashi da ƙarfi da ikon ƙara kuɗin Man fetur take.
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya data koma ta sake nazarin hanya mai bullewa don magance matsalar, ɗaya daga cikin hanyoyin acewarsa shine a magance matsalar ƙarfin Dalar Amurka akan tattalin arzikin Najeriya.
Falana ya kuma ce al’ummar Najeriya zasu kalubalanci wannan tsari yana mai cewa mafita akan matsalar Man Fetur ya kunshi na doka da kuma siyasa.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.