Labarai

An Kama Jirgin Ruwa Da Ya Saci Mai Daga Najeiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin  karfafa tsaro a duk fadin kasar nan domin dakile matsalar satar mai, mako guda bayan da aka tsare wani babban jirgin ruwa a gabar tekun Equatorial Guinea.

Shugaba Buhari yace, baza’a bar wasu tsirarun ‘yan fashi bata gari su na satar danyen man da Allah ya albarkaci Najeriya ba, don haka ne ma ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta dakatar da ayyukan wadannan barayin a yankin Neja Delta.

Buhari ya kara da cewa, “Bai kamata a rika baiwa irin wadannan masu aikata laifuka makafaka ba, tare da bukatar karfafa hadin gwiwa da kasashe makwabta wajen dakile wadannan aika-aika.

Kalaman shugaba Najeriya Muhammadu Buhari na zuwa ne, bayan da sojojin ruwan Equatorial Guinea suka kama wani jirgin ruwa mai suna MV Heroic Idun dake daukar gangan mai miliyan uku, kwanaki kadan bayan ya tsarewa jami’an tsaron Najeriya.

Babban mai shigar da kara na kasar Equatorial Guinea, Anatalio Nzang Nguema, ya shaidawa gidan talabijin na kasar TVGE cewa, an kama ma’aikatan jirgin su 25 — da suka hada da Indiyawa 16 da ‘yan kasar Sri Lanka bakwai, da wani dan kasar Poland sai kuma dan kasar Philippines.

Ana sace miliyoyin ganga kowace rana a Najeriya, kasar da ta fi kowacce kasa samar da danyen mai a Afirka, inda ake sayar da su a kasuwannin bayan fage.

Leave a Reply