Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da Éullar cutar anthrax a kasar a hukumance.
Wata sanarwa da maâaikatar noma da raya karkara ta ce an kai rahoton dabbobin da ke nuna alamun yiwuwar kamuwa da cutar anthrax a wata gona da ke Suleja a Jihar Neja zuwa ofishin babban jamiâin kula da dabbobi na Najeriya a ranar 14 ga watan Yuli.
Maâaikatar ta ce lamarin ya faru ne a wata gonar dabbobi da ta Æunshi shanu da tumaki da awaki da ke Gajiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a Æaramar hukumar Suleja a jihar Neja, inda wasu daga cikin dabbobin ke da alamomi da suka haÉa da zubar jini daga sassan jikinsu, hanci, idanu da kunnuwa.
Ta ce tawagar masu bayar da agajin gaggawa da ta haÉa da Æwararrun maâaikatan lafiya na tarayya da na jihar sun ziyarci gonar don gudanar da bincike na farko tare da tattara samfurori daga dabbobin da suka kamu da cutar.
Ma’aikatar ta ce gwaje-gwaje na Cibiyar Nazarin Dabbobi ta Æasa ta tabbatar da kamuwa da cutar, “wanda ke nuna alamar cutar anthrax ta farko a Najeriya a cikin ‘yan shekarun nan”.
Ta yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta yi gargaÉi ga âyan Najeriya makonnin da suka gabata bayan samun labarin Éarkewar cutar anthrax a Arewacin Ghana inda duk dabbobin da suka kamu da cutar suka mutu.
Sanarwar ta Æara da cewa gwamnati ta yi kira ga Æ´an Najeriya da su gaggauta kai rahoton bullar dabbobin da ke zubar da jini a jikinsu ga hukumomin kiwon lafiyar dabbobi ko kuma maâaikatan aikin gona.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








