Labarai

Da Dumi-Dumi: Ƴan sanda Sun Kama Shugaban NLC A Imo

 

Jami’an tsaro sun cafke Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero a Owerri, babban birnin Jihar Imo.

Benson Uper, shugaban yada labarai na NLC, ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Uper ya ce, ‘yansanda ne suka yi awon gaban da Ajaero daga sakatariyar NLC, suka kai shi inda ba a sani ba.

A ranar 30 ga Oktoba, NLC ta yi alkawarin dakatar da ayyukan ma’aikata a Imo daga ranar 1 ga watan Nuwamba, don nuna rashin amincewa da take hakkin ma’aikata.

Jaridar Leadership

About the author

Muhammad Sani Abdulhamid