Latest:
Labarai

Mutum 4,387 sun mutu a haɗurran mota a wata shidan farko na 2023 a Najeriya

 

Jimillar mutum 4,387 ne suka mutu sakamakon haɗurran ababen hawa cikin wata shidan farko na 2023 a Najeriya, a cewar hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa.

Jami’in faɗakarwa na hukumar Federal Road Safety Corps (FRSC), Bisi Kazeem, ya faɗa wa kamfanin labarai na Najeriya NAN cewa daga watan Janairu zuwa Yunin 2023 an samu mutum 14,108 da suka ji raunuka.

A lissafi na tsakatsaki, alƙaluman na nufin mutum 731 ne ke mutuwa duk wata, ko kuma 24 a kowace rana, a cewar rahoton na NAN.

“Waɗannan haɗurra na faruwa ne saboda tafiya cikin dare, da gajiya, da karya dokar hanya, da wucewar ganganci, da amfani da tayoyin da suka gama aiki, da kuma tsananin gudu,” in ji Mista Kazeem.

“Ka san kuma jami’anmu ba su aiki cikin dare, saboda haka ne direbobi ke amfani da wannan damar wajen karya dokokin tuƙi.”

BBC Hausa

Leave a Reply