Latest:
Labarai

Shugaba Tinubu zai yi jawabi wa ƴan Najeriya a yau

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ƴan ƙasar jawabi a yau Litinin.

Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa na shugaban Dele Alake ya fitar, ta ce shugaban zai yi jawabin ne da misalin karfe 7 na yamma.

Sanarwar ta kuma buƙaci dukkan gidajen talabijin da rediyo da su haɗa tashoshinsu da Gidan Talabijin na Tarayya NTA da kuma Rediyon Tarayya FRCN domin watsa jawabin ga ƴan ƙasa.

BBC Hausa

Leave a Reply