Latest:
Labarai

Tinubu ya naɗa Dr.Olayemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan CBN

 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sunan Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) na tsawon shekara biyar, da zarar Majalisar Dattijan ƙasar ta amince da shi.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, yau Juma’a.

Bayanin ya ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakin ne bisa dogaro da sashe na 8 (1) na dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007, wadda ta bai wa shugaban ƙasar karfin ikon naɗa shugaba da mataimaka huɗu na Babban Bankin.

Sanarwar ta kuma bayyana sunayen wasu mutane huɗu da shugaban ya amince da su domin naɗawa a matsayin mataimakan gwamnan babban bankin na Najeriya.

Mataimakan su ne:

(1) Mrs. Emem Nnana Usoro

(2) Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo

(3) Mr. Philip Ikeazor

(4) Dr. Bala M. Bello

Shugaban ya buƙaci waɗanda aka naɗan su mayar da hankali wajen aiwatar da muhimman sauye-sauyen da aka ɓullo da su a bankin a ƙoƙarin gwamnatinsa na sake fasalin tattalin arziƙin ƙasar.

A watan Yunin wannan shekara ne shugaban ƙasar ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ƙasar ta ce an dakatar da Emefiele ne ne domin gudanar da bincike da kuma kasancewa wani ɓangare na ƙoƙarin sauya fasalin harkokin kuɗi a ƙasar.

Kwanaki kaɗan bayan dakatar da shi ne rundunar tsaron ciki ta ƙasar, DSS ta tabbatar da kamawa tare da tsare tsohon gwamnan babban bankin.

DSS ɗin ta kuma gurfanar da Emefiele a gaban kotu bisa tuhumar sa da laifuka daban-daban.

BBC Hausa

Leave a Reply