Labarai

Wata mata ta roki kotu ta raba auren ta da mijin ta bisa naɗa mata na jaki kullum

 

Wata matar aure mai suna Rashidat Ahmed ta kai karar mijinta Yusuf zuwa kotu a Igboro dake Ilorin ranar Laraba inda ta ke rokon kotun ta raba auren ta saboda yawan duka da cin fuska da mijinta ke yi mata.

Rashidat ta ce sun haifi ‘ya’ya uku amma ta hakura da auren saboda ba za ta iya daure wa cin zarafin da ya ke mata ba.

Ta ce lokuta da dama mijinta kan lakada mata dukan tsiya saboda bata yi girki ba alhalin shine bai bata kudin cefane ba.

Rashidat ta ce yakan watsar mata da kayanta a waje yana koranta ta koma gidan iyayenta a duk lokacin da suka samu rashin jituwa a tsakanin su.

“A dalilin wata harkalla da Yusuf ya aikata, Yan sanda sun tsare ni na makonni biyu a caji ofis, ban ji ba ban gani.

Yusuf ya roki kotun da kada ta raba auren saboda yana da matarsa.

Ya musanta duk hujojin da Rashidat ta bada a kotun a kansa amma ya ce kwanaki biyu matarsa ta yi a ofishin ‘yan sanda ba makonnin biyu ba.

Yusuf ya yi alkawarin cewa ba zai kara dukar matarsa ba.

Alkalin kotun Aminullahi AbdulLateef ya roki Rashidat da ta yi hakuri ta yafe wa mijinta.

Ya Kuma hori Yusuf da ya zama miji da Uba na gari daga yanzu.

AbdulLateef ya daga shari’a zuwa ranar 20.

Premium Times Hausa

Leave a Reply