Latest:
Labarai

Yadda Ɗan Autan Sarkin Kano Ado Bayero mai shekaru 22 ya auri Mata 2 a lokaci guda

Dan autan Mai Martaba Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero mai kimanin shekaru 22, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar.

Mustapha Bayero, wanda ke fama da ciwon huhu, shi ne da na karshe ga marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero.

An daura auren Yarima Mustapha da kyawawan matansa guda biyu, Badi’a Tasiu Adam da Fatima Ibrahim Adam a Masallacin Markaz Imamu Bukhari, Rijiyar Zaki da Masallacin Juma’a na Tsakuwa, Kano.

A lokacin da marigayi sarkin Kano Alh Ado Bayero yana raye akan dora yarima Mustapha a cikin keken dokin doki a lokutan hawan sallah.

Leave a Reply