Labarai

Kenya na fama da karancin kwaroron roba 

Kenya na fama da karancin kwaroron roba da take rabawa kyauta ga maza saboda ragin tallafi da take fuskanta daga kungiyoyi. Ƙasar na bukatar akalla kwaroron roba miliyan 400 a kowacce shekara.

Gwamnati a yanzu na iya raba kwaroron roba miliyan 150 ne kacal, wanda bai kai rabin abin da ake bukata ba.

Gidauniyar AIDS Foundation, ta yi gargaɗin cewa idan ba a shawo kan matsalar ba, Kenya na iya fuskantar kalubalen yaɗuwar cututtuka irinsu HIV, da cutar da ke yaɗuwa ta jima’i da ɗaukar cikin da ba a so.

Wani babban jami’i a hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ya ce akwai bukatar ɗaukan matakai a cikin gaggawa.

Ƙwararru a fannin lafiya da ‘yan majalisa da ƙungiyoyin tallafi za su gudanar da wani taro nan da kwanaki uku a birnin Mombasa domin shawo kan matsalar da kuma samar da karin magungunan HIV.

BBC Hausa

Leave a Reply