Labarai

Malamin islamiyya ya ce ga garinku bayan shan duka a wajen surukansa a Neja

 

Wani malamin islamiyya, Malam Umar Tasi’u ya yi gamo da ajalinsa sanadiyyar dukan tsiya da wasu surukansa suka lakada masa a Jihar Neja.

Wani makwabcin marigayi Malam Tasi’u, ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne yayin da mamacin ya je ganin ’ya’yansa biyu a gidan tsofaffin surukansa bayan ya rabu da uwarsu.

A cewar majiyar, harzuka da sakin ’yarsu da ya yi ne ya sanya da zuwan malamin suka daure shi da igiya suka lakada masa na jaki har sai da ya ce ga garinku nan.

“Ya je ganin ’ya’yansa biyu wadanda suke hannun tsohuwar matarsa a gidan iyayenta da ke layin Landan a Minna.

“Sai kawai surukansa suka kama shi suka daure, sannan suka lakada masa duka har sai da ajali ya yi kira.

“An kawo mana gawarsa da Yammacin Asabar, kuma washegari Lahadi muka yi jana’izarsa da misalin karfe 10:00 na safe.

Aminiya ta tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun wanda ya tabbatar da mutuwar malamin.

Sai dai ya ce wasu bata-gari ne suka kai masa harin da ya yi ajalinsa.

“Da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar 22 ga watan Oktoba muka samu rahoton kisan gilla a ofishinmu da ke Unguwar GRA.

“A rahoton, mun samu cewa da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar 21 ga watan Oktoba ne wani Umar Tasi’u, mazaunin Unguwar Daji ya gamu da ajalinsa a hannun wasu bata-gari da suka kai masa hari a Layin Landan da ke birnin Minna.

“Sun yi masa jina-jina kuma ana mika shi Asibitin IBB da ke Minna ya ce ga garinku nan.

“Yanzu haka wannan lamari yana hannunmu kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin kama wadanda ake zargi da aika-aikar,” a cewar DSP Abiodun.

Jaridar Aminiya