Labarai

Nijar ta rufe sararin samaniyarta da iyakokin ƙasar

 

A jamhuriyar Nijar, wa’adin da ƙungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin da sukai juyin mulki a Jamhuriyar Nijar na su koma barikokinsu da maida mulki ga farar hula ko su ɗauki matakin soji, ya cika ba tare da sun bi umarnin ba.

Gwamnatin sojin Nijar ta sanar da rufe sararin samaniyar ƙasar, da kuma shirin kare iyakokin ƙasar na kasa. Wakiliyar BBC ta ce “Mun sa ran kungiyar Ecowas za ta fitar da wata sanarwa daidai lokacin da wa’adin ya cika, ko matakin da za ta dauka nan gaba, amma shiru ka ke ji.”

Kawunan mambobin ƙungiyar ECOWAS ya rarrabu kan ɗaukar matakin sojin, inda Nigeria da Ivory Coast suka kafe kan lallai a dawo da mulki hannun shugaba Muhammad Bazoum, su kuwa Mali da Burkina Faso ke goyon bayan sojojin da sukai juyin mulkin.

BBC Hausa

Leave a Reply